ZAbatool naturalle

Barka da zuwa Zabatoolnaturalle shafin mu na hausa inda zaku koyi hanyoyin dazaku bi don gyaran jiki da abubuwa na asali

HANYOYIN DA ZA A BI DON MAGANCE BUSHEWA DA TSAGEWAR KAFA

Published September 2, 2020. 11:12am. By Fatimah batool. Under Gyaran fata

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/09/2425/20200902-103957.png
Kula da tafin kafa yana da mutukar mahimmanci especially lokacin iska zaki ga kafa yana bushewa yana Cracking sometimes ma harda jini. wasu kuma koba ma lokacin iska ba koda yaushe kafar su cikin bushewa yake.
GA HANYOYIN MAGANCE WANNAN MATSALAR :
- Da farko dai ya kamata ki ringa tsaftace tafin kafan ki. kina yawan wankewa kina goge shi.
- Ki ringa yawan shafa mai.
- ki ringa sa slippers Kar ki ringa taka datti.
- ki ringa yawan sa socks in zaki fita.
- Ki ringa yawan shan ruwa.
- sannan kuma ki ringa sa lalle a tafin kafan ki.
GA ABUBUWAN DA ZAKI AMFANI DA SU DON MAGANCE TSAGEWAR KAFA
1. ki sami ruwan dumi ki zuba a cikin bahun sai ki zuba gishiri, glycerine, rosewater sai ki tsoma kafarki yayi 20min sai ki sa dutsan goge kafa ki goge. in kin gama sai ki shafa Vaseline.
2. ki tsoma kafar ki a ruwan dumi for 15mins sai ki goge kafan da dutsen goge kafa sai ki cire kafar daga ruwa ki goge da towel sai ki shafa pure vaseline ki sa socks. kiyi hakan kullum in zaki kwanta da daddare.
3. ki zuba Zuma a cikin ruwan dumi sai ki tsoma kafar ki yayi 15min sai ki cire. ko kuma ki shafa zuman yayi 15mins sai ki wanke kafar da ruwan dumi. zai miki maganin tsagewar kuma yayi taushi.
4. Coconut oil yana magani tsagewar tafin kafa sosai bayan kin tsoma kafar ki a ruwan dumi na 20min sai ki goge kafan da towel Sai ki shafa Coconut oil kisa socks da daddare.

Share this on:

Be the first to comment on "HANYOYIN DA ZA A BI DON MAGANCE BUSHEWA DA TSAGEWAR KAFA"

Publish Comment

Name:

Email Address:

Comment:

Game da Mai Wallafa

I'm Fatima Batoola, bahaushiya mai Son ado da Kwalliya


Related Posts

  • [Post thumbnail] YADDA ZAKI KULA DA FARCENKI
    Idan kina so ki samu nails masu kyau, masu shining kuma Lafiyayyu Wanda basa kakkaryewa basu da wani rauni ko tabo a jikinsu. Sai ki bi wa innan Han...Read more
  • [Post thumbnail] Yadda zaki sami fata mai kyau
    Idan kikabi wa innan Hanyoyin inshaAllah zaki ga chanji a fatar ki 1. Yawan shan ruwa kamar 6-8 cups a rana 2. yawan shafa mai kar a ringa bari ji...Read more
  • [Post thumbnail] YADDA ZAKI MAGANCE TABON FUSKA
    Idan kina fama da tabon fuska wanda hakan ya faru ne sakamakon mutuwar kuraje da suka fito a fuska. to ki zabi daya daga cikin wa'innan hanyoyi don...Read more